Zaɓe ya ƙarato a France
April 18, 2007Yan takara neman shugabancin ƙasar Fransa, sun shiga gangarar ta ƙarshe a yaƙin neman zaɓe.
Ya zuwa yanzu daga yan takara 12 da ke buƙatar maye gurbin shugaba Jaquces Chirak , 4 a ke kyauttata zatan za su taka rawar gani a zagayen farko, na zaɓen da za a gudanar ranar lahadi mai zuwa.
Wannan yan takara sun haɗa da, Nikola Sarkozy na jami´ yar UMP, mai riƙe da ragamar mulki, sai kuma Segolene Royal ta Jam´iyar PS, na ukun,su shine, Fransois Bayrou na jam´iyar FDN mai matsakaicin ra `ayi, sannan Jean Marie Le Pen, na jam´iyar FN mai aƙidar nuna ƙyamar baki, wanda wani mataki na ba zata, ya kara a zagaye na 2, tare da shugaba mai barin gado Jaques Chirac a zaɓen shekara ta 2002.
Sanarwa daga opishin ministan cikin gida, a birnin Paris, ta bayyana cewar, komai ya kammalla a shirye-shiryen wannan zaɓe, hatta a ƙasashen ƙetare, inda kussan Fransawa dubu ɗari 9, za su kaɗa ƙuri´a.