1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawayen Libiya na ci gaba da samun nasara

August 20, 2011

'Yan tawayen Libiya suka ce a yanzu suna da cikakken iko da birnin Brega -mai tashar teku

https://p.dw.com/p/12Kb9
'Yan tawayen Libya akan hanyar su ta zuwa Zawiya ranar 13.08. 2011.Hoto: dapd

A wannan Asabar ce 'yan tawayen ƙasar Libiya suka yi da'awar cewar sun karɓe cikakken iko da birnin Brega, mai tashar teku, kana suna nausawa kusa da birnin Tripoli, fadar gwamnatin Libiya. Tashar telebijin ta Larabci, wato Alhazeera, ta ruwaito cewar karɓe iko da birnin na Brega ya baiwa 'yan tawayen damar samun iko akan wasu muhimman na'urorin sarrafa man fetur dake birnin, baya ga wata matatar man fetur da suka ƙwace a garin Zawiyah kwanaki biyun da suka gabata.

A halin da ake ciki kuma, wani na hannun daman shugaban Libiya Muammar Gadhafi mai suna Abdel-Salam Jalloud ya sauya sheƙa zuwa wani yankin dake hannun 'yan tawayen a tsibirin dake yammacin ƙasar ta Libiya. Jalloud dai ya taɓa kasancewa mutum na biyu mafi ƙarfin faɗa-aji a cikin gwamnatin Libiya, kana abokin shugaba Gadhafi daya taimaka masa wajen ɗarewa kan mulki a lokacin juyin mulkin shekara ta 1969. Hakanan Jalloud ya riƙe muƙamin firaministan Libiya a shekarun 1970.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita Halima Balaraba Abbas