1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawayen Libiya na buƙatar wani sabon juyin-juya-hali

December 14, 2011

Ana ci gaba da fama da faɗa da saɓani a ƙasar Libiya, inda dubban-dubatar mutane suka fara zanga-zangar nuna rashin gamsuwarsu da salon kamun ludayin shuagabannin ƙasar

https://p.dw.com/p/13SbO
Masu zanga-zanga a Bengazi
Masu zanga-zanga a BengaziHoto: dapd

Tun a 'yan kwanakin da suka wuce dubban-dubatar mutane ke zanga-zangar nuna adawa da majalisar riƙon ƙwarya da shugabanta Mustafa Abdel Jalil tare da kiran neman 'yancin faɗin albarkacin baki da kuma hana tsaffin jami'an gwamnatin Ghaddafi samun wasu muhimman mukamai a al'amuran ƙasar Libiya. Gaba ɗaya ma dai suna kiran gabatar da wani sabon mataki na juyin-juya-hali kuma cibiyar zanga-zangar har yau ita ce Benghazi dake gaɓar tekun gabacin ƙasar. Su dai masu alhakin juyin-juya-halin na ganin cewar a yanzu wani koƙari ake yi a mayar da su saniyar ware, a maimakon an shigar da su domin cin gajiyar nasarar borensu, in ji Andreas Dittmann, ƙwararren masani akan al'amuran Libiya a jami'ar Giessen dake nan Jamus:

"Maganar ta shafi matasa ne daga gabacin Libiya, abin da ya haɗa har da mata masu tarin yawa, waɗanda su ne suka fara gabatar da matakin wannan juyin juya halin kuma a yanzu aka yi watsi dasu a yayinda a ɗaya hannun tsaffin jami'an gwamnati ke daɗa samun ƙaƙƙrfan matsayi. Wannan ci gaba, ba shakka ba alheri ba ne ga makomar zaman lafiyar ƙasar."

epa03032029 Libya's National Transitional Council (NTC) chairman Mustafa Abdul Jalil speaks during a press conference In Tripoli, Libya, 12 December 2011. Reports stated that hundreds of Libyans gathered in Benghazi, eastern Libya, to protest against Abdul Jalil and the NTC, calling for more transparency and the trial of former regime_s officials. EPA/SABRI ELMHEDWI
Shugaban majalisar wucin gadin Libiya Mustafa Abdel JalilHoto: picture-alliance/dpa

Andreas Dittmann ya ƙara da cewar, muddin masu juyin-juya-halin Libiyan suka lura da cewar ba wani banbanci tsakanin sabuwa da tsofuwar gwamnatin da aka kifar, to kuwa ana iya shiga wani hali irin shigen na ƙasar Masar domin gabatar da wani sabon juyin-juya-hali na biyu a Libiyan. Suma dai ƙungiyoyin fafutukar kare haƙƙin ɗan-Adam na suka a game da yadda sabbin shuagabannin Libiyan ke tafiyar da al'amuran ƙasar a cikin duhu. Majalisar riƙon ƙwarya ta ƙasa ta gabatar da wasu dokoki, waɗanda har yau mutane ba su da wata cikakkiyar masaniya game da su, in ji Fred Abrahams daga ƙungiyar kare haƙƙin ɗan-Adam ta Human Rights Watch.

To sai dai kuma ba zanga-zangar ta baya-bayan nan ce ke yin nuni da mawuyacin halin da Libiya ke ciki dangane da makomar zaman lafiyarta ba. Domin kuwa har yau ana ci gaba da fuskantar bata kashi da zub da jini tsakanin dakarun wasu sassan da ba su ga maciji da juna a ƙasar. A ma ƙarshen makon da ya wuce sai da aka fuskanci musayar wuta tare da hafsan-hafsoshin sabuwar rundunar sojan Libiyan, wanda ya tsallake rijiya da baya. Kazalika a ranar litinin da ta wuce an fuskanci arangama da asarar rayuka da dama a kudancin Tripoli, fadar mulkin Libiya. An ma ƙiyasce cewar akwai dakarun ko-ta-kwana kimanin 120 da suka rufa wa Ghaddafi baya, waɗanda kuma ke fafutukar samun wani muhimmin matsayi a ƙasar yanzu haka, in ji Andreas Dittmann:

"Matsalar dake akwai shi ne kasancewar bayan kawo karshen yakin basasar an shiga wawason makamai a sansanonin soja da sauran rumbunan makaman kasar ta yadda duk wani mai iko zai nemi da ya mallaki makami a hannunsa, ƙwance ɗamarar waɗannan makaman shi ne ya kamata a ba wa fifiko to kafin lamarin ya zama gagara-badau."

Men with the National Transitional Council show confiscated heavy artillery at and NTC warehouse in Tripoli *** Bilder von DW-Mitarbeiter Don Duncan, Tripoli, Dez. 2011
Makamai sun barbazu hannun mutaneHoto: DW

Ko da yake a fafutukar neman tabbatar da zaman lafiyar Libiya, Mustafa Abdel Jalil ya sanar cewar a cikin watanni uku masu zuwa za a canza tsare-tsaren sojan ƙasar a kuma rarraba ma'aikatun gwamnati a birane dabam-dabam, amma wani muhimmin abu bisa manufa kuma shi ne a gabatar da sahihan matakan da zasu taimaka a ɗinke ɓarakar dake akwai tsakanin al'umar Libiyan kamar dai shari'ar masu laifukan keta haddin ɗan-Adam ƙarƙashin mulkin Ghaddafi. Amma wannan alhaki ne da ya rataya a wuyan su kansu mahukuntan ƙasar, ba kafofin shari'a na ƙasa da ƙasa ba.

Mawallafi: monika Dittrich/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Usman Shehu Usman

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani