'Yan tawayen ƙungiyar Seleka sun shiga birnin Bangui
March 23, 2013Talla
Shaidun gani da ido sun ce sojin gwamnati da dakarun 'yan tawaye sun gwabza fada gabannin shiga birnin, kazalika mazauna garuruwan da ke daura da birnin na Bangui sun ji harbe-harben manyan bindigogi da kuma tashin bama-bamai.
Kawo yanzu dai ba a tantance yawan yankunan da 'yan tawayen yanzu haka su ke rike da su ba tun bayan da su ka samu shiga birnin na Bangui a wannan Asabar din.
'Yan tawayen na Seleka dai wanda su ka lashi takobin hambarar da gwamnatin kasar sun sake daukar makamai a wannan makon ne bayan da su ka yi ikirarin cewar shugaban kasar Francois Bozize ya saba alkawurun da ya yi mu su na sanya wasu daga cikin dakarunsu a rundunar sojin kasar.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman