1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Tawaye na ƙasar Libiya na ci-gaba da samun galaba

June 28, 2011

Dakarun ƙungiyar 'yan tawaye na ƙasar Libiya sun ƙwace wata ma'ajiya ta makamai daga cikin hannu sojojin kanal Muammar Gaddafi

https://p.dw.com/p/11kmN
Dakarun 'yan tawaye na LibiyaHoto: AP

'Yan tawaye na ƙasar Libiya sun ƙwace wata ma'ajiyar makamai ta gwamnatin kanal Gaddafi dake a kudancin kasar cikin hamada wacce ke da nisan kilomita 120 daga birnin Tripoli.Masu aiko da rahotannin na kamfanin dilancin labaran na Faransa AFP sun ce 'yan tawaye cikin tankokin yaƙi sun isa a garin wanda ke maƙare da man'yan rubunna na makamai wanda gwamnatin Libiya ta ajiye.

Kuma an yi musayar wuta tsakanin sassan biyu kafin daga bisani dakarun gwamnatin su arce.Masu lura da al'amura na cewa wannan kamen ma'ajiyar makamai da 'yan tawayen suka yi nasar a kai,zai ƙarama su ƙarfin guiwa a kokarin da suke yi na ƙara danawa zuwa birnin Tripoli.

A ɗaya hannu kuma Gwamnatin ƙasar Libya ta yi watsi da sammacin da kotun shari'ar manyan laifuka ta ƙasa da ƙasa dake Hague ta bayar na cafke shugaban Libyan Muammar Gaddafi. kotun ta bada sammacin kamo Gaddafi da 'yayansa da suka hada da Saif al-Islam bisa zargin aikata laifukan cin zarafi da keta haddin bil Adama. Da take baiyana sammacin mai shari'ar Sanji Masenono Monageng ta yi bayani da cewa -

" Tace kama Muammar Gaddafi da Saif al-Islam Gaddafi ya zama wajibi a daidai wannan lokaci domin gurfana gaban kotu da kuma tabbatar da cewa basu cigaba da yin amfani da karfin iko wajen yin tarnaki ga binciken da ake gudanarwa musamman wajen rufe tabargazar da jami'an tsaron ƙasar suka aikata.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Usman shehu Usman