1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkawa a kasashen waje na zaben shugaban kasa

Abdullahi Tanko Bala
April 27, 2023

Turkawa miliyan daya da rabi da ke zaune a Jamus na kada kuri'a a zaben shugaban kasarsu da yan majalisun dokoki a mazabu 16 da gwamnatin Jamus ta amince da su

https://p.dw.com/p/4Qdji
Deutschland | Beginn der Türkei-Wahlen
Hoto: Rolf Vennenbernd/dpa/picture alliance

Zaben wanda za a fara zagayen farko a ranar 14 ga watan Mayu a Turkiyya zai kasance abin da manazarta ke gani a mtasayin zakaran gwajin dafi mai tsauri ga shugaba Recep Tayyip Erdogan wanda ya shafe shekaru 20 a karagar mulki.

Kasar ta amince Turkawa da ke zaune a kasashen waje su kada kuri'a a zaben shugaban kasa da na majalisar dokokin tarayya. Za kuma a ci gaba da zaben har zuwa  ranar 9 ga watan Mayu a mazabu 16 da gwamnatin Jamus ta amince da su a fadin kasar.

Turkawan da ke zaune a Jamus sun kai miliyan daya da rabi wadanda suka cancanci kada kuri'a.

Wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a baya bayan na nuni da yiwuwar yin kankankan tsakanin Erdogan da babban mai kalubalantarsa Kamal Kilicdaroglu wanda ke jagorantar kawancen jam'iyyun da suka tsame addini da ayyukan gwamnati da jam'iyyar ra'ayin rikau da kuma 'yan kishin kasa.