1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron masana da masu kare muhalli

Umaru AliyuNovember 26, 2007

Masana sun yi nazarin hanyoyin kare muhalli da rage yawan zafi a yanayin sararin samaniya

https://p.dw.com/p/CTR8
Rajendra Pachauri da Ban Ki MoonHoto: AP

A Ƙarshen shawarwari na misalin mako guda a Valencia, hukumar ƙasa da ƙasa mai kula da batun yanayi, wato IPCC a taƙaice, ta gabatar da rahoton ta na huɗu, kuma na ƙarshe a game da yanayin sararin samaniya. Babban abin da aka maida hankali kansa a cikin rahoton, shine yadda ake kara samun dimamar duniya, sakamakon aiyukan yau da kullum na dan Adam.

Masana da masu ilimin kimiyya kimanin dubu biyar ne suka taimaka aka tsara rahoton game da yanayin sararin samaniya da aka gabatar a ƙarshen taron na Valencia, wanda kuma wakilai daga kimanin ƙasashe ɗari da hamsin suka yi nazarin sa, suka kuma tsara shi yadda zasu gabatarwa shugabannin siyasa na ƙasashen su. Shugaban hukumar ta kare yanayi, Rajendra Pachauri yace wannan rahoto an amince dashi ne amma ba sulhu aka cimma game dashi ba.

Wannan dai rahoto ne na masana ilimin kimiyya, kuma a ƙarshe waɗanda suka rubuta wnnan rahoto sune suke da alhakin amincewa ko ƙin amincewa da sharhunan da zasu fito daga bakin yan siyasa. Ganin cewar wannan rahoto na masana kimiyya za a gabatar dashi ne ga ‚yan siyasa da suke da alhakin yanke kudiri kansa, saboda haka wajibi ne a rubuta gaskiyar halin da ake ciki yadda yan siyasar zasu fahimce shi. Hakan kuwa babu abin da ya danganta shi da tattaunawa kann rahoton.

TO amma duk da haka, sai da aka ɗauki lokaci mai tsawo ana shawarwari kafin a amince da rahoton, dake ƙunshe a shafi ashirin da ukku. Sakon da rahoton ya ƙunsa a fili yake: yanzu dai ana fuskantar wani yanayi ne inda ake fama da canjin yanayin sararin samaniya da dan Adam ya jawowa kansa da hannun sa, bisa dukkan alamu ta hanyar fitar da hayaƙi dake gurbata yanayi. Rahoton yace ana iya kaiyade ƙaruwar zafi a duniya baki daya, amma ba za a iya gabatar dashi gaba daya ba. Tsananin barnar da za a samu ga rayuwar dan Adam, inji rahoton zai dogara ne ga karfin matakan da za a dauka a kokarin magance wannan matsala ta ɗimamar yanayi. Hukumar ta kare yanayia tayi hangen cewar idan aka sami nasarar rage yawan haraji da ƙasashe suke fitarwa dake gurbata muhalli, ana kuma iya samun nasarar rage canjin da ake samu a yanayin sararin samaniya. Pachauri yace:

Wannan dai abu ne mai muhimmanci da aka gano. Idan har ana da shirin daukar wani mataki, to kuwa wannan mataki tilas ya shafi sadaukar da kai. Hakan yana nufin wajibi kenan a fara gina masana’antu da basa fitar da hayaƙi mai yawa dake gurbata muhalli.

Hakan kuwa yana nufin wajibi kenan ayi watsi da hanyoyin makamashi na al’ada, kamar kwal da man fetur da gas, wanda kona su da masana’antu ke yi yakan haddasa fitar da hayaƙi mai yawa dake zama illa ga yanayin sararin samaniya. Sai dai ba ko wace kasa ce take farin ciki da gaskiyar wannan hali ba. ƙasar Saudi Arabiya mai arzikin man fetur alal misali, ita ce tafi haddasa cikas a shawarwarin da aka yi na kokarin tsara rahoton da yan siyasa zasu fahimta, su kuma amince dashi. Tawagar wakilan Jamus ta nuna cewar burin ta shine ta ƙaiyade ƙaruwar ɗimamar yanayi da misalin awo biyu kawai a ma’aunin zafi da sanyi. ƙaramin minista a ma’aikatar kare muhalli ta taraiya, Michael Müller yace wannan shi ya kamata ya zama burin duka mahalarta taron kare muhalli za a yi a Bali.

To amma shugaban hukumar kare yanayi ta ƙasa da ƙasa, Rajendra Pachauri yace ba gwmanatoci kaɗai ba, suma jama’a ana bukatar taimako da goyon bayan su a matakan da kare kewayen dan Adam. Yace wajibi ne jama’a ya zama sune masu aiwatar da canje-canjen da suke ƙaunar ganin sun samu a duniya.