1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin jagoran 'yan tawayen ƙasar Libiya

September 1, 2011

Mustafa Abdul Jalil mai shekaru 59 ya taɓa riƙe muƙamin ministan shari'a na Libya, kafin ya shiga tawaye bayan ɓarkewar boren ƙin jinin gwamnatin Gadhafi.

https://p.dw.com/p/12Reg
Mustafa Abdul Jalil, shugaban majalisar wucin gadi na Libya.Hoto: picture-alliance/dpa

Shi dai jagoran 'yan tawayen Libiya ba wani ba ne illa Mustafa Mohammed Abdul Jalil, tsohon ministan shari'ar da ya raba gari da Moammar Gadhafi tun ma kafin guguwar neman sauyi ta kaɗa a cikin ƙasar. Hasali ma dai ɗarewa kan kujerar majalisar wucin gadi da a baya ke da cibiya a birnin Bengazi da Jalil ya haska sunansa a ciki da wajen ƙasar ta Libiya. Alhali ya shafe shekaru da dama ya na alƙalanci a Tripoli, tare da ma zama babban mai shigar da ƙara na babban birnin ƙasar. To sai dai ko da a shekarar 2007 zuwa 2011, lokacin da ya riƙe muƙamin ministan shari'a na tsawon shekaru huɗu, madugun 'yan tawayen, Mustafa Abdul Jalili bai taɓa zama cikakken ɗan amshin shatan Kanal Moammar Gadhafi ba. Maimakon haka ma sai ya yi ta ƙoƙarin yaɗa manufofi na karan kansa, tare da neman karesu.

Mustafa Abdul Dschalil und Franco Frattini
Mustafa Abdul Dschalil, da ministan wajen Italiya Franco FrattiniHoto: picture-alliance/dpa

Lokaci da ya yi hannu riga da manufofin Gadhafi

Jagoran 'yan tawayen na Libiya da aka haifa a shekarar 1952 a garin el Beida ya fara takun saƙa da Moammar Gadhafi a shekara ta 2009, a inda ya amince cewar tsare fursunoni 300 da ake yi a gidan yarin ƙare kukanka na Abu salim ba tare da yanke musu hukunci ba ya saɓawa doka. Tun daga wannan lokaci ne Mustapha Mohammed Abdul Jalil ya fara nisanta kansa da manufofin shugaba Moammar Gadhafi. Ko da a shekara ta 2010 sai da ya sake tsokaci dangane da wajibcin gurfanar da fursunonin na Abu Salim gaban ƙuliya, ko kuma a sake su ba tare da wani ɓata lokaci ba. Sai dai gwamnati ta nuna adawarta da duk wani mataki na aiwatar da tunanin Abdul Jalil. Wannan dalilin ne ma, jagoran 'yan tawayen na Libiya ya dogara a kai wajen yin murabus daga mukaminsa na ministan shari'a. Lamarin da ya haifar masa yabo tsakanin ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da suka himmatun wajen kare hakkin bil Adama ciki kuwa har da Amnesty International, duk kuma da ƙin amincewa da murabus ɗin Abdul Jalil da kanal Gadhafi ya yi.

Der libysche Revolutionsführer Muammar al-Gaddafi
Moammar Gadhafi, lokacin da ya ke rike da madafun mulkin LibyaHoto: AP

Lokacin da Abdul Jalili ya raba gari da gwamnatin Libiya

Bayan da aka tayar da boren nuna adawa da gwamnatin Moammar Gadhafi a tsakiyar watan fabrairu na shehrara ta 2011 ne, Mustafa Abdul Jalil ya juya wa gwamnati baya, tare da haɗa kai da 'yan tawaye a cibiyar su ta birnin Benghazi inda ya kafa majalisar wucin gadi. Tun daga wannan lokaci ne dai Mustafa Abdul Jalil ya yi ta amfani da duk wata dama da ta samu wajen shafa wa hukumomin Libya kashin kaji. Ko da a cikin wata hira da aka yi da shi lokacin da ake tsakiyar faɗa tsakanin 'yan tawaye da kuma dakarun gwamnati, sai da Abdul Jalil ya yi gargadi game da halayen shugaba Gadhafi na rashin sanin ya kamata.

"ƙwarai kuwa mun san halin Moammar Gadhafi. Ba ya ɗaukan Libiya da kuma al'ummar ƙasar da wani mahimmanci. A shirye ya ke ya banka wa birnin Tiripoli wuta. Kana zai yi ɗana makamai a cikin motoci. Kazalika zai iya amfani da sinadarin gas. Mun san cewar zai iya aiwatar da kowanne daga cikin munanan manufofinsa. Saboda haka muna nan a cikin shiri."

Rebellen in Libyen
Murnar 'yan tawayeb Libya bayan nasara a kan dakarun GadhafiHoto: AP

 Goyon bayan NATO da duniya ga Mustafa Abdul Jalil

To dai Mustafa Abdul Jalil ya yi amfani da ƙudirin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta zartar a watan Maris na shekata ta 2011 wajen neman dakarun NATO su aiwatar da dokar hana shawagin jiragen sama, wanda daga bisani aka rikiɗa shi zuwa tallafa wa 'yan tawaye a yunƙurin da suka kira na kare fararen hula daga musgunawar gwamnatin Gadhafi. Sannu a kan hankali  'yan tawayen suka yi ta mayar da biranen ƙasar ta Libiya ɗaya bayan ɗaya ƙarkashin ikonsu, har lokacin da suka shiga Tripoli babban birnin ƙasar, tare da hamɓarar da gwamnatin Moammar Gadhafi. Yayin da a ɗaya hannun majalisar wucin gadi bisa jagorancin Mustafa Abdul Jalil ta yi ta samun amincewar ƙasashen yammacin duniya ciki kuwa har da Faransa da Ingila a matsayin halartaciyar gwamnatin ƙasar ta Libya. Suma dai wasu ƙasashe na duniya sun bi sahun takwarorinsu na yamma wajen amincewa da majalisar ta wucin gadi bisa jagorancin Mustafa Abdul Jalili, bayan da 'yan tawaye suka mamaye birnin Tripoli.

Sai dai kuma Mustafa Abdul Jalil ya gargaɗi 'yan tawaye da su guje wa ɗaukar fansa akan dakarun gwamnati. Ya na mai cewar idan ko suka yi amfani da wannan dama wajen cin zarafin magoya bayan Moammar Gadhafi, to ba shakka zai yi murabus daga muƙaminsa na shugaban majalisar wucin gadi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Usman Shehu Usman