Taɓa Ka Lashe: 27.10.2010
October 28, 2010Talla
A cikin kwanakin baya-bayan nan maganar sajewar baƙi a Jamus ta ƙara yin zafi, inda ake kira gare su da su mayar da hammi wajen koyan harshen Jamusanci a matsayin matakin farko na cimma manufar da aka a gaba. Taimakawa yaran baƙi tun a makarantun nasare domin su naƙalci harshen Jamusanci zai ba da gagarumar gudunmawa bisa wannan manufa.