Simone Bagbo matar tsohon shugaban Côte d'Ivoire na shirin fuskantar kotun kasa da kasa
December 4, 2012
A wana ganawar da yayi da masu hannun da shuni a wannan Talatar,praministan Côte d'Ivoire Daniel Kablan Ducan,ya ce kawop yanzu ba a dauki wata kwakwarar shawara ba a kan matsayin matar tsohon shugaban kasar Laurent Bagbo a dangane da bukatar aikata kotun kasa da kasa da ke hukunta manyan laifufuka da ke da cibiyarta a birnin Hage. A shekara ta 2011 ne kotun ta bada samacin cafke Simone Bagbo da ake zargi da hannu a rikicin kasar da ya biyo bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar wanda kuma ya yi sanadiyar mutuwar kimanin mutane dubu 3.
A shekara ta 2011 ne hukumomin kasar suka tusa keyar mijinta a kotun ta kasa da kasa,to saidai kawo yanzu ba a yanke masa hukunci ba,a zargin da ake masa na hura wutar rikicin da ya barke a kasar.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Zainab Mohamed Abubakar