1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Turkiyya zai gana da takwaransa na Azerbaijan

Binta Aliyu Zurmi
September 24, 2023

Shugaba Racep Tayyip Erdogang na Turkiyya zai gana da takwaransa na kasar Azerbaijan bisa rikicin yankin Nagarno-Karabakh da aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

https://p.dw.com/p/4WkVW
Aserbaidschan Baku | Präsident Ilham Alijew hält Fernsehansprache
Hoto: Press Service of the President of Azerbaijan Ilham Alijew/REUTERS

Sanarwar da mahukuntan Ankara suka fidda na nuni da cewar babban batun da shugabannin biyu za su tattauna a kai shi ne batun rikicin yankin Nagarno-Karabakh.

Gwamnatin Turkiyya ta jima tana goyon bayan sojojin Azerbaijan, musamman ma a wannan sabon rikicin.

A daya hannun kuwa al'ummar Armeniya ne suka bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta hanzarta tura dakarun wanzar da zaman lafiya yankinsu domin saka ido a kan yancinsu da ma tabbatar musu da tsaro, bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da ma jingine makamai da aka fara a ranar Juma'ar da ta gabata.

Wannan na zuwa ne bayan da a jiya Asabar gwamnatin kasar Azerbaijan ta yi wa duniya alkawarin kiyaye hakkokin Armeniyawa mazauna yankin Nagorno-Karabakh, yanki da takaddama ta yi zafi a tsakaninta da kasar Armeniya.