1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Sri Lanka ya yi murabus

July 15, 2022

Bayan kwashe lokaci na neman shugaban Sri Lanka da ya yi murabus, a karshe Shugaba Rajapaksa ya sanar da ajiye aikin nasa kuma tuni aka rantsar da shugaba na riko.

https://p.dw.com/p/4EAFZ
Sri Lanka | Wirtschaftskrise - Rücktritt Präsident Gotabaya Rajapaksa
Hoto: Rafiq Maqbool/AP Photo/picture alliance

Kakakin majalisar dokokin Sri Lanka ne ya tabbatar da murabus din Shugaba Gotabaya Rajapaksa a hukumance.

Murabus din ya zo bayan kwashe lokaci 'yan Sri Lankan na zanga-zangar neman shugabannin gwamnatin kasar da su yi adabo da mulki saboda karuwar wahalhalu.

Mr. Rajapaksa ya bayyana murabus dinsa a rubuce daga Singapore ta sakon Email da ya aike wa kakakin majalisar dokokin kasar, kafin daga bisani a aiko da takardar da ya sanya wa hannu.

TWannan ne dai karo na farko da wani shugaba ke murabus a Sri Lanka tun lokacin da kasar ta rungumi tsarin mulki na shugaba mai cikakken iko a 1978.

A halin da ake ciki dai an rantsar firaministan Sri Lankan Ranil Wickremesinghe a matsayin shugaban kasa na riko, kafin a majalisar ta zabi sabon shugaba cikin kwanaki bakwai.

Yanzu dai miliyoyin 'yan kasar baki har kunne da samun labarin murabus din tsohon Shugaba Gotabaya Rajapaksa wanda ya yi kaurin suna wajen murkushe 'yan tawayen Tamil Tigers da suka addabi kasar a baya.