Shugaban Askarawan Libiya ya yi marabus
June 9, 2013Talla
Majiyoyin gwamnati a ƙasar ta Libiya sun ce Al Mangush ya miƙa takardarsa ta marabus ga Majalisar Dokokin wace tuni ta amince da buƙatar.
Shekaru biyu dai bayan mutuwar kanal Gaddafi tsohon shugaban na Libiya har yanzu gwamnatin ta gaza aiwatar da shirin kwance ɗamarar tsofin mayaƙan 'yan tawayen abin da ke zaman babban cikas ga sha'anin tsaro. Masu aiko da rahotannin sun ce babban jami'in sojin na nuna rashin amincewar sa da tsarin aikin kula da harkokin tsaro da hukumomin suka ƙaddamar tun lokacin da suka karɓi ragamar mulki. A jiya ne dai wasu ɗarurruwan matasan suka gudanar da zanga zanga a birnin Benghazi da zumar neman a kwance ɗamarar tsofin mayaƙan.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh