Shugaban kasar Vietnam ya mutu
September 21, 2018Talla
An dau lokaci ana rade-raden tsananin rashin lafiyar da shugaban ke fama da shi, musamman tun bayan da aka shugaban na ziyartar likitoci a kasashen waje. Wasu 'yan kasar sun ce rabon da su ga shuganan tun shekarar 2017 loakcin da ya halarci liyafar cin abinci da tawagar kasar Chaina da suka ziyarci kasar.
A shekara ta 2016 ne marigayin ya dare karagar mulki, inda shugabannin manyan kasashen duniya kamar Donald Trump suka ziyarce shi kasar a zamaninsa. A yanzu mataimakiyarsa Dang Thi Ngoc Thinh za ta shugabanci kasar kamar yadda dokokin kasar suka tanada kamin majalisar dokoki ta zabi sabon shugaban kasa a watan gobe na Oktoba.