Za kuji cewar shugaba Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiyya yayi wata ganawa ta musamman da shugaban gwamnatin kasar Libya wanda Majalisar Dinkin Duniya ta aminta da shi, daidai lokacin da tsamin dangantaka ke kara kamari tsakanin sojojin Turkiyya da kuma masu goyon bayan mahukuntan kasar Libya.