A cikin shirin za a ji cewa Hukumomin tsaro a Najeriya da suka hada da na kwastam da shige da fice da rundunar sojin sama da na kasa sun tsaurara tsaro akan iyakokin kasar a wani mataki na dakile hanyoyin da masu fasakwauri suke shigar da kayayyaki cikin kasar ta barauniyar hanya.