A cikin shirin an ji cewar an gudanar da jana'izar tsohon shugaban Zimbabuwe Robert Mugabe kana an ji cewar an gudanar da zaben shugaban kasa Afghanistan sai dai jama'a da dama basu fita kada kuri'a ba saboda irin kalubalen tsaro da ake fuskanta da kuma barazanar da 'yan Taliban suka yi na kai hare-hare lokacin zaben.