Shirin na kunshe da matsalolin da labaran boge ke haddasawa a Najeriya da kiran da shugabannin jam'iyun adawa suka yi a nijar ga Shugaban Mahamadou Issoufou na ya sauka daga kan mulki. Ana samun rudani a tsakanin al'umma a kasashe masu amfanin da kudi na CFA bayan taron da kasashe mambobin kungiyar ECOWAS a Abuja.