A cikin shirirn za a ji a Jamhuriyar Nijar jami'an kafofin yada labaai masu zaman kansu sun shiga wani halin fargaba bayan wani yunkurin gudanar da zaman dirshan a bakin ofishin ministan sadarwa inda jami'an tsaro suka afka masu. A share guda kuwa jami'an tsaro suka janye a gidan talbajin mai zaman kansa wato TV Labari da yake rufe tun ranar Lahadi.