1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'ar Seif al-Islam a birnin Zintan

August 23, 2012

A cikin watan Satumba ne hukumomin ƙasar Libiya za su fara shari'ar ɗan marigayi shugaba Gadhafi.

https://p.dw.com/p/15vWo
In this image taken from new video which has become available Tuesday Nov. 22, 2011, showing of Moammar Gadhafi's son Seif al-Islam examines his injured hand, in video taken shortly after his capture on Saturday Nov. 19, 2011, at a safe house in the town of Zintan, Libya. The video shows Seif al-Islam arguing with his captors and admonishing them saying that Libya's regions that were united in revolution will turn against each other in the near future and rip the country apart. Seif al-Islam says his hand was injured during a recent allied bombing. (Foto:APTN/AP/dapd) TV OUT
Hoto: dapd

Hukumomi a ƙasar Libiya sun sanar da cewar a cikin watan Satumban dake tafe ne za su gurfanar da seif al-Islam, ɗan marigayi tsohon shugaban Libiya Mouamer Kadhafi a garin Zintan, inda ake ci gaba da tsare shi tun cikin watan Nuwamban bara.

Kakakin mai gabatar da ƙara na gwamnatin ƙasar ta Libiya Taha Nasser Baara ya ce wani kwamiti daga ofishin babban mai shigar da ƙarar ya kammala binciken laifukan da Seif al-Islam ya aikata tun lokacin fara juyin-juya-hali a cikin watan Fabrairun shekara ta 2011, kuma ya shirya tuhumce-tuhumcen da ake yiwa Seif al-Islam ɗin. Ya ce nan da kwanaki ƙalilan masu zuwa ne ofishin mai gabatar da ƙarar zai amince da zarge-zargen, kana ya sanya ranar fara sauraren shari'ar a cikin watan Satumba.

Idan za a iya tunawa dai kotun sauraren manyan laifukan yaƙi ta ƙasa da ƙasa da ke birnin the Hague na ƙasar Holland ta miƙa sammacin gurfanar da Seif al-Islam bisa zargin cin zarafin jama'a, amma sabbin mahukunta a ƙasar Libiya sun tsaya kai da fatar cewar za su gudanar da shari'ar sa ne a ƙasar sa ta haihuwa.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe