Sakamakon zaɓen cika gurbi a Libanon
August 6, 2007Talla
Ministan cikin gidan ƙasar Libanon, ya bada sakamakon zaɓen cika gurbin yan majalisar dokoki da aka gudanar jiya jiya a wasu yankuna guda 2 na ƙasar.
A Mertn an fafata tsakanin tsofan shugaban ƙasa Amine Gemayel, da kuma ɗan takara jam´iyun adawa Camille Khoury, mai goyan bayan madugun yan adawa Michel Aoun.
Sakamakon da a ka bayar ya nunar da cewa, tsofan shugaban ƙasar ya sha kayi, to saidai tuni, ya bayyana ƙinamin cewa da shi, wanda ya ce akwai maguɗi a cikin sa.
A yakin Beyruth dantakakara jam´iyun adawa, Momahed Amine Itani ya lashe zaɓen.
An gudanar da wannan zaɓɓuɓuka 2, domin cike gurbin yan majalisar dokoki 2, da su ka rasa rayuka a cikin wasu hare-haren ta´danci, wato Walid Eido da kuma Pierre Gemayel.