1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Matakin gaba kan rigakafin corona na AstraZeneca

April 7, 2021

Hukumar kula da magunguna ta Tarayyar Turai ta ce ba kasafai ake samun illar dunkulewar jini ba ga wadanda aka yi wa allurar rigakafin corona na kamfanin AstraZeneca.

https://p.dw.com/p/3rhEA
AstraZeneca Impfstoff
Hoto: Soumyabrata Roy/NurPhoto/picture alliance

A rahoton karshe kan binciken, daraktar hukumar Emer Cooke ta shawarci jama'a kan ci gaba da amfani da rigakafin don yakar annobar ta COVID-19. 

Bisa kwararan hujojjin bincike na kimiyya, ta ce allurar na da matukar amfani kana ta na ceto rayuka da dama, kazalika hukumar ba ta sanya wasu dokoki kan allurar ba koma kayyade shekarun wadanda za a yi wa.

Zurzurfan binciken hukumar dai na zuwa ne baya da kasashen Turai da dama suka dakatar da amfani da allurar rigakafin corona na kamfanin AstraZeneca a watan da ya gabata bisa zargin haifar da daskarewar jini ga wadanda aka yi wa.