1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saif al-Islam ya kaurace daga Libiya

October 25, 2011

Rahotanni sun ce Saif al Islam dan marigayi kanar Gaddafi na hanyar zuwa jamhoriyar Nijar domin samun mafaka

https://p.dw.com/p/12ypP
Saif al-Islam GaddafiHoto: AL ARABIYA

Rahotannin na nuni da cewa, dan Marigayi Kanar Gaddafi Saif al Islam wanda daa aka sa ran zai gaji mahaifinsa a mulkin na Libiya na kan hanyarsa zuwa jamhoriyar Nijar inda wadansu kanensa suka riga suka koma, domin samun mafaka bisa bayanan da wasu jami'an gwamnati suka bayar.

Rissa ag Boula wani mashawarcin shugaban kasa kuma zababben mamba a majalisar yankin Agadez ya fadawa kamfanin dillancin labarun AP ta wayar tarho cewa yayi magana da wasu 'yan kabilar Tuareg wadanda suka tabbatar masa da cewa suna taya Saif al islam shigowa kasar ta Nijar. Boula ya kuma bayyana cewa Saif wanda kotun hukunta laifuka ta kasa da kasa ke neman sa bisa dukkan alamu yana kokarin ratsawa ta cikin Aljeriya domin shiga kasar ta Nijar. To sai dai Boula ya kara da cewa idan har ya isa gwamnatin zata karbe shi amma duk da haka wajibi ne ta mutunta dokokin kasa da kasa ko da shike wannan shawara ce da zai yanke da kansa. Saadi Gaddafi da sauran wadanda suka rike manyan mukamai a gwamnatin Gaddafi suna cigaba da samun mafaka a Nijar inda aka yi masu daurin talala a wani gida dake birnin Yamai.

Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita:Umaru Aliyu