1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon bayani game da harin ta'addanci a Libiya

September 20, 2012

Saɓanin ikirarin da hukumomin Libiya suka yi tunda farko, Amirka ta ce harin daya rutsa da jami'an diflomasiyyar ta tsautsayi ne.

https://p.dw.com/p/16BlT
US President Barack Obama (L) delivers the State of the Union address to a joint session of Congress on Capitol Hill in Washington DC, USA, 27 January 2010. The State of the Union address comes one year and one week after Obama took office. President Obama is speaking on a wide variety of issues such as the federal deficit, unemployment, health insurance reform, campaign contributions and foreign policy. EPA/MIKE THEILER
Hoto: picture-alliance/dpa

Wani babban jami'in gwamnatin Amirka ya shaidawa majalisar dokokin ƙasar cewar ko da shike harin daya janyo mutuwar ma'aikatan jakadancin Amirka a birnin Benghazi na ƙasar Libiya na ta'addanci ne amma akwai yiwuwar ba tsara shi ba aka yi. A dai wannan Larabar ce darektan kula da cibiyar yaƙi da ayyukan ta'addanci ta ƙasar Amirka Matthew Olsen ya shaidawa 'yan majalisar dokokin ƙasar wannan bayanin, inda ya ƙara da cewar ko da shike harin na ta'addanci ne amma bayanan da suke da shi ya zuwa yanzu na nuni ne da cewar maharan sun yi amfani da damar ce kawai wajen kai harin, amma ba wai sun tsara ne tun gabannin lokacin ba, sai dai kuma ya ce Amirkar na ci gaba da gudanar da binciken.

Idan za'a iya tunawa dai -jim kaɗan bayan ƙaddamar da harin daya janyo mutuwar jakadan Amirka a ƙasar Libiya Chris Stevens da wasu ma'aikatan ofishin jakadacin Amirka ukku a birnin Benghazi ne shugaban majalisar dokokin ƙasar ta Libiya ya ce tsara harin aka yi, tun gabannin boren nuna ƙyamar Film na ɓatanci ga manzon Allah Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu