1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin ƙabilanci na ci-gaba da addabar Libiya

February 15, 2012

Shekara guda bayan ƙaddamar da boren da ya kifar da gwamnatin Muammar Gaddafi a Libiya, rikicin ƙabilanci ya zama ruwan dare a ƙasar.

https://p.dw.com/p/143n1
Men chant slogans during an anti-Syrian regime protest in front of the Chinese embassy in Tripoli, Libya, Monday, Feb. 6, 2012. Russia and China have vetoed a U.N. Security Council resolution aimed at ending Syria's bloodshed, despite international outrage over a devastating bombardment of the city of Homs by President Bashar Assad's forces. The veto and the show of support by Russia last Saturday raised concerns that Assad's regime could now unleash even greater violence to crush the revolt against his rule, assured that his ally would prevent international action while continuing its weapons sales to Damascus. (Foto:Abdel Magid al-Fergany/AP/dapd)
Hoto: dapd

A daidai lokacin da mahukuntan a Libiya ke shirye shiryen bikin cika shekara ɗaya da yin juyin juya halin da ya hamɓarar da gwamnatin Muammar Gaddafi da kuma fara shigar da 'yan tawayen dake riƙe da makamai cikin dakarun sojin ƙasar, faɗace faɗacen ƙabilanci na ci gaba da addabar ƙasar.

Ko shakka babu, har yanzu akwai jan aiki gaban mahukuntan Libiya wajen dawo da doka da oda a ƙasar da yaƙi ya kacaccala watanni biyar bayan kisan gillar da aka yi wa kanal Gaddafi. Yadda matasa 'yan bindiga daɗi da suka yi ruwa suka yi tsaki wajen kifar da gwamnatin Gaddafi, a yanzu ke ɗaukar doka a hannunsu, yadda suke amfani da bakin bindiga kan abin da bai taka kara ya karya ba, abin da ke kaiwa ga faɗace-faɗacen ƙabilanci da ya zama kusan ruwan dare game duniya a ƙasar. Ko a ranar Talata ma sai da fiye da mutane ashirin suka halaka yayin bata kashi tsakanin ƙabilun Tabow da Zuwayya a garin Kufra dake gabacin ƙasar.

Wannan na zuwa ne a yayin da aka shiga halin ɗarɗar a ƙasar bayan fara bukukuwan cikar shekara ɗaya da juyin juya hali a ƙasar, yadda shugaban sojojin ƙasar Yusuf Almankush ya buƙaci duk wanda ke riƙe da makami da ya bada sunansa cikin sojojin gwamnati ko ya miƙa makaminsa nan da ranar juma'a.

FILE - In this Sept. 18, 2011 file photo, former rebel fighters celebrate as smoke rises from Bani Walid, Libya, at the northern gate of the town. Moammar Gadhafi loyalists seized control of a Libyan city and raised the ousted regime's green flag, an official and military commanders said Tuesday, Jan. 24, 2012, in the most serious revolt yet against the country's government. (Foto:Alexandre Meneghini, File/AP/dapd).
Hoto: AP

"Ku zo mu yi aiki tare ƙarƙashin doka don kafa dakarun da za su samar da cikakken tsaro domin yanzu lokacin yaƙi ya kare."

Matsalar tsaro a Libiya bata taƙaita kan waɗannan matasa ba, kamar yadda Muhammad Shawush, wani jami'in tsaro a garin Zawiya ke faɗi.

"Saɓanin yadda wasu kafofin watsa labarai ke yaɗawa, kan cewa ana yaƙin basasa a Libiya, ba haka abin yake ba. Abin dake faruwa shine, ƙoƙarin kakkaɓe baragurbin magoya bayan Gaddafi ake yi."

Kadan dai za'a tuna, a makwannan ne, Sa'adi Gaddafi, yayi barazanar jagorantar sabon tawaye a ƙasar, yadda yace yana da dubban magoya baya dake cikin shirin ko ta kwana don fatattakar waɗanda ya kira 'yan fashi daga ƙasar.

Mai yiwa irin wannan kashedi da magoya bayan Gaddafi ke yi, ya sanya jami'an tsaron ƙasar suka hana al'adar da mutanan ƙasar ta Libiya suka saba ta harba bindiga sama yayin bukukuwa, don kar ɓata gari su yi ɓarna.

Libyans damage the car of National Transitional Council (NTC) Chairman Mustafa Abdel Jalil, to express their dissatisfaction towards the policy of the Council in governing the country, in Benghazi January 21, 2012. People in Benghazi, birthplace of the revolt which forced out former Libyan leader Muammar Gaddafi, have been protesting for weeks to demand the sacking of Gaddafi-era officials and more transparency about how the NTC is spending Libyan assets. REUTERS/Esam Al-Fetori (LIBYA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Hoto: Reuters

Hakanan su ma dangin waɗanda suka rasa rayukansu a yaƙin ƙasar za su iya kawo tangarɗa a bukukuwan saboda barazanar shirya zanga-zangar nuna fushinsu ga hukumar wucin gadin ƙasar da suka ce mayaudara da bayan sun ci moriyar ganga suke jefarwa da kwaurenta.

Ga dukkan alamu dai matuƙar sabin mahukuntan na Libiya ba su aiwatar da doka ba ji ba gani ba da kuma kwatanta adalci ga 'yan ƙasar fiye da wanda Gaddafi ya yi musu ba, wankin hula zai kaisu dare.

Mawallafi: Mahmoud Yaya Azare
Edita: Mohammad Nasiru Awal