Rikicin ƙabilanci a Libiya ya janyo asarar rayuka
March 27, 2012Aƙalla mutane 30 aka kashe sannan sama da 100 aka ji wa rauni a cikin kwanaki biyu na wani rikicin ƙabilanci da ya ɓarke a birnin Sabha dake kudancin ƙasar Libiya. Likitoci a yankin sun faɗa wa kamfanin dillancin labarun AFP cewa waɗanda suka rasu 'yan ƙabilu ne dake yaƙar ƙabilar Toubou masu ɗaukar makami dake a birnin na yankin hamada mai nisan kilomita 750 kudu da Tripoli babban birnin ƙasar. Sai dai shugaban ƙabilar ta Toubou Issa Abdel Majid Mansur ya ce 'yan ƙabilarsa 40 aka kashe, kuma ya zargi mahukuntan Libiya da amfani da jiragen saman yaƙi da motocin sulke akan wuraren 'yan Toubou dake kudancin birnin na Sabha. Shugaban rundunar tsaron ƙasa a yankin, Kanal Mohammed Bussif ya ce ana cikin wani hali mai sarƙaƙƙiyya a yankin, inda ya zargi wasu ɓatagari dake samun goyon bayan ƙasashen ƙetare.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadisou Madobi