1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici ya ki ci ya ki cinyewa a Libiya

June 13, 2012

Siyasar ramuwar gayya da ta cimmma manufa ta addini sun kama hanyar yin kaka gida a Libiya

https://p.dw.com/p/15DLK
Source News Feed: EMEA Picture Service ,Germany Picture Service A vehicle mounted with an anti-aircraft gun is seen on the tarmac at Tripoli's international airport in this still image taken from video June 4, 2012. Clashes broke out between rival Libyan militias at Tripoli's international airport on Monday after angry gunmen drove armed pickup trucks on to the tarmac and surrounded planes, forcing the airport to cancel flights. REUTERS/Reuters TV (LIBYA - Tags: CIVIL UNREST POLITICS TRANSPORT)
Hoto: Reuters

Har yanzu gwamnatin Libiya na fuskantar kalubale daga biranen Bengazi da Al-Kufra da Zintan da rikice-rikice suka ki ci suka ki cinyewa a cikinsu. Akwai kuma barazanar fuskantar wani kalubalen daga yankin Abzinawa da ke arewa maso yammacin kasar.

A birnin Bengazi da ke gabashin kasar Libiya an fuskanci mutuwar tsohon shugaban ma'aiktar cikin gida Muftah al-Urfi bayan da ya samu rauni mai tsanani a cikin harin da aka kai masa a lokacin da yake fita daga masallaci. A baya ga haka a yan kwanaki da suka gabata an kai hare-hare akan jami'an Amirka da kuma ayarin motocin ofishin jakadancin Birtaniya da ke a wannan birni. Ana kuma samun rahotannin da ke nuni da sake barkewar fada a garin Al-Kufra dake yankin kudu maso gabashin kasar inda mutane 17 suka mutu a wani fada da ya barke tsakanin bakar fata 'yan kabilar Toubou da mayakan sauran kabilu.

Halin rashin sanin tabbas

Professor Andreas Dittman, masanin halayyar dan Adam kuma kwararren masani akan Libiya ya bayyana dalilan da suka sa har yancu kura ta lafawa a Libiya.

Men from Bangladesh, who used to work in Libya and fled the unrest in the country, carry their belongings as they arrive in a refugee camp at the Tunisia-Libyan border, in Ras Ajdir, Tunisia, Wednesday, March 9, 2011. The 20,000-capacity transit camp for thousands of migrant workers who have fled the fighting in Libya in the past two weeks is about seven kilometers (four miles) from the Libyan border and is expanding with each day of crisis in Libya. (Foto:Lefteris Pitarakis/AP/dapd)
Masu gudun hijra daga LibiyaHoto: dapd

"Ga baki daya akwai maganar rashin natsuwa. A hakika hakan ta shafi rashin sanin tabbas game da yadda za a tinkari 'yan adawa wadanda ake kallo a matsayin masu nuna goyon baya ga Muammar Gadhafi. Dalili na biyu shine tashe-tahshen hankulan da aka fuskanta a daiden wannan lokaci a garin Al- Kufra inda mata da kananan yara suka rasa rayukansu."

Wata matsalar kuma ita ce tsare Melinda Taylor jami'ar kotun hukunta laifukan yaki ta ICC da ake ci gaba da yi a Libiya bisa mallakar wasu bayanai na sirri akan dan Gadhafi, wato Saiful Islam da yanzu haka ke tsare a garin Zintan. Prof. Andreas Dittman ya ce sharadin da gwamnatin Libiya ta gindaya domin sakin wannan jami'a na daga cikin abubuwan da ke jefa kasar cikin hali na rashin tabbas

"An tsare jami'an kotun ICC ne bayan da suka kai wa saiful Islam ziyara a gidan yari. Dalili kenan da ya sa ake zargin Melinda Taylor da laifin leken asiri. Wannan na daya daga cikin manyan zargi-zargin da ake samu daga gwamnatin Libiya."

A matsayin sharadinta na sakin Melinda Taylor gwamnantin Libiya ta bukaci jamaiar da ta nuna inda wani na hannun damar Sailful Islam ke fake.

In this undated photo provided by the International Criminal Court (ICC), Australian defense lawyer Melinda Taylor poses for a photograph at an unknown location. The International Criminal Court demanded the release on Saturday, June 9, 2012 of four of its staffers, including Taylor, which it says are being detained in Libya, where they are part of an official mission sent to meet with the imprisoned son of deposed dictator Moammar Gadhafi. (Foto:ICC/AP/dapd)
Melinda TaylorHoto: dapd

Raunin gwamnatin Libiya

Bugu da kari dukan masu ruwa da tsaki a kasar ta Libiya suna amfanin da raunin da gwamnatin ke da shi. Wannan na daga cikin abubuwan da ke kara tsunduma kasar ta Libiya a cikin rikici kamar yadda Andreas Dittman ya nunar.

"Hakan na da nasaba ne da tabarbarewar tsaro da ake fuskanta bayan hambarar da Muammar Gadhafi. Kabilanci da addinin da kuma aika-aikar 'yan bata gari na daga cikin dalilan da ke janyo aukwar hare-hare da rikice rikice. To amma dukan masu ruwa da tsaki suna amfani da raunin da gwamnati ke da shi wajen kara shigar da kasar a cikin halin ni ya su."

Dittman ya yi misali da halin da ke wakana a Al-Kurfa a matsayin abin da ke kara dagula lamura a kasar. Wata matsalar kuma ita ce rukunoni dabam- dabam na sojojin sa kai masu manufar ramuwar gayyya da ake da su a garin Zintan da ke yankin Arewa maso yamacin kasar. Sai kuma uwa uba matsalar 'yan kishin Islama da suka dade da samun gindin zama a Bengazi.

Za a iya sauraron sautin wannan rahoto daga kasa.

Mawallafi: Guenther Birkenstock/ Halima Abbas
Edita: Abdullahi Tanko Bala

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani