Rigingimun kabilanci sun haddasa salwantar rayuka a Libiya
February 21, 2012Wata arangamar da ta barke tsakanin wasu kabilu biyu a yankunan da ke kudu maso gabashin saharar Libiya, ta yi sanadiyyar rayuka fiye da 100 a tsukin kwanaki goman da suka gabata.
Majiyoyi sun tabbatarwa kamfanin dillancin labarun Faransa wato AFP cewa akalla mutane 113 daga kabilar Toubu da kuma wasu 20 daga kabilar zwai suka mutu a wani gari mai suna Kufra tun da kabilun suka fara fada tsakaninsu a ran 12 ga watan Fabrairu. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jagorar gwamnatin rikon kwaryar kasar ya ce gwamnatin bata da karfin shawo kan 'yan tawayen da ke nuna turjiya wajen mika makamansu, tun bayan da suka kifar da gwamnatin marigayi Kanar Gaddafi, a yunkurin da ta keyi na kafa gwamnati mai karfi a kasar wacce ke da arzikin man fetur.
A wata hira da yayi da kamfanin dillancin labarun Associated Press, Mustafa Abdul Jalil ya yi gargadin cewa zai dauki tsawon lokaci kafin sabbin shugabanin na Libiya, su iya daidaita matsalolin cin hanci da karbar rashawa, da rashin yardar da suka gada daga mulkin tsohon shugaban mai rasuwa na tsawon shekaru fiye da 40.
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Yahouza Sadissou Madobi