Rashin tabbas a dangantakar Larabawa da kasashen Turai
February 26, 2019A wannan sharhi da Bernd Riegert ya rubuta, ya ce yankunan biyu suna da sabani babba kamar yadda muradunsu suka rarraba.
Bernd Riegert ya fara da tambayar shin taron kolin da ya gudana tsakanin Kungiyar tarayyar Turai da kasashen Larabawa holoko ne kawai babu wani abu a cikinsa ko taron shan shayi?
Ya ce a fakaice kusan haka abin yake saboda babu wasu shawarwari ko matakai kwarara da aka gani a jadawalin taron na farko tsakanin kungiyar tarayyar Turai da kasashen Larabawa. To amma babu wanda ya tsammaci haka.
Babban makasudi haduwar ta farko shi ne ganawa da juna da kuma shata jadawalin tattaunawa a gaba. An yi ganawar ta diflomasiyya a Sharm el Sheikh, sai dai kuma ta gudana ne ba tare da samun karsashi da aka yi fatan gani da zai kai ga cimma burin kudirorin da aka sanya a gaba ba.
Sai dai kuma duk da haka an duba muhimman batutuwan yakin basasa da suke ciwa kasashen Siriya da Yemen tuwo a kwarya. An kuma bada shawarwari kan yadda za a samar da daidaito da kwanciyar hankali a kasr Libya.
Amma ba hurumin kungiyar Tarayyar Turai ba ne ko kawancen kungiyar kasashen Larabawa da ba ta da karfin tasiri ta iya aiwatar da wani abu.
Kasar Masar wadda ta karbi bakuncin taron ta fayyace cewa bata aminta da shawarar kungiyar tarayyar Turai ba na yin sansanin dakatar da yan cirani daga Afirka na tsawon lokaci ba a kasar. Wannan batu dai ya fayyace yadda bangarorin biyu na Kungiyar tarayyar Turai da kuma kasashen Larabawa ke bukatar juna.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ma kara da baiyana wannan mataki da cewa yana da muhimmanci ga dorewar makomar kungiyar Tarayyar Turai.