1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha na iya kawo karshen rikicin Ukraine

Pinado Abdu WabaFebruary 5, 2015

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya bayyana cewa shugaba Vladimir Putin na Rasha zai iya dakile rikicin Ukraine idan har ya na so

https://p.dw.com/p/1EWHk
Ukraine Kiew John Kerry und Arsenij Jazenjuk
Hoto: picture-alliance/dpa/Sergey Dolzhenko

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shugabanin Turan da suka hada da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da takwaranta na Faransa Francois Holland suke shirin zuwa Mosko domin tattaunawa da mai rike da madafun ikon Rashar a fadan Kremlin.

John Kerry ya kuma yi kira ga duk bangarorin da su tsagaita wuta, yayin da ya ke jawabi bayan ya tattauna da shugaban kasar Ukraine Petro Poroschenko, ya kuma yi kira ga Rashar da ta ba da hadin kai wajen ganin an cimma maslaha ga rikicin cikin kwanciyar hankali da diplomasiya.

" Wajibi ne a jajirce a yanzu, a tsagaita wuta ba a kan takarda ko fatar baki kadai ba, amma a bi shi da aikatau ma'anan a janya manyan makamai daga yankunan da aka riga aka tsagaita wuta, daga kan iyaka, kuma daga duk wani layin da za a iya harba makamai masu dogo ko matsakaicin zango yadda za su kasance da lahani ga fararen hula.