Praministan Mali ya kai ziyara a kasar Tchadi
December 4, 2012Talla
Shugaban gwamnatin rikon kwarya na Mali Check Modibo Dirra,ya kai wata ziyara a kasar Tchadi inda ya gana da shugaban kasar Idriss Deby Itno da kuma shugaban Tarayyar Afrika bugu da kari shugaban jamhuriyar Benin Thomas Bony Yayi a wani matakin neman kwarin gwiwa ga daukacin kasashen Afrika da su nuna bukatar samun izini daga Majalissar Dinkin Duniya domin aikawa da dakarun kasa da kasa a arewacin Mali inda 'yan kishin islama suka mamaye watani 9 da suka gabata.
Bony Yayi ya kira Majalisar Dinkin Duniya da ta gaugauta ceto al'ummar arewacin Malin daga mawuyacin halin da suke ciki sakamakon cin zarafin da kuma azabar da suke gani da sunan musulunci.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi