1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Pakistan: Kotu ta jingine daure Khan

Abdullahi Tanko Bala
August 29, 2023

Kotun daukaka kara a Pakistan ta jingine hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari da wata kotu a kasar ta yanke wa tsohon firaminista Imran Khan.

https://p.dw.com/p/4ViRQ
Pakistan | Zanga zanga kan tsare Imran Khan
Pakistan | Zanga zanga kan tsare Imran KhanHoto: Asif Hassan/AFP/Getty Images

Ko da yake zai sake gurfana a gaban kotu a nan gaba domin bitar shari'ar, hukuncin kotun daukaka karar zai bai wa Khan mai shekaru 70 da haihuwa damar shiga takara a zaben majalisun dokoki da ke tafe.

Karin bayani

Tsohon firamnista ya daukaka kara

Khan ya musanta dukkan zarge zargen da ake yi masa inda ya ce bai karya kowace doka ba.

A watan nan ne dai wata kotun Pakistan: Kotu ta daure Imran Khan Pakistan ta daure Imran Khan kan laifin boye wasu kadarori bayan sayar da kyaututtukan da ya karba wadanda aka bai wa kasar a lokacin da yake kan karagar mulki kuma ta yanke masa hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari.

Babbar kotun ta Islamabad ta kuma bada belin Khan sai dai babu tabbas ko za a sako shi saboda yana fuskantar wasu tarin kararraki tun bayan kawar da shi a karagar mulki sakamakon kuri'ar yankar kauna da yan majalisar dokoki suka kada masa a watan Afrilun 2022.