Napoli ta hana 'yan wasanta buga gasar AFCON
August 3, 2022Talla
Mamallakin kungiyar kwallon kafar Napoli ta kasar Italiya Aurelio De Laurentiis ya ce daga yanzu ba zai sanya hannu a kan kwantaragi da wani dan kwallo na Afirka ba har sai dan wasan ya amince a rubuce cewa ba zai shiga gasar kwallon kafar Afirka ta AFCON ba.
Dan wasan Senegal Kalidou Koulibaly wanda yanzu ke a kungiyar Chelsea da dan Kamaru Andre Zambo Anguissa na cikin 'yan wasan Afirka da suka rasa wasannin kungiyar Napolin a farkon shekarar nan a sakamakon wakiltar kasashensu da suka yi a gasar kwallon kafar Afirka ta AFCON.