Bama-bamai sun tashi daga jikin gawa
February 27, 2019An gano yadda bayan kisan wani manomi, 'yan bindiga suka dasa bama-bamai a jikin gawarsa kafin su kai ta gidan mahaifansa. Ba zato ba tsanmani, bama-baman suka tashi a daidai lokacin da jama'a ke tsakiyar jimamin kisan gillar da aka yi wa mutumin. Daga cikin wadanda harin ya rutsa da su har da iyayen mamacin da wasu danginsa. Lamarin ya kasance irinsa na farko da aka taba gani inji wani jami'in tsaron kasar ta Mali.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas, ke ziyarar aiki a kasar ta Mali, Maas ya ce aikin samar da tsaro da rundunar wanzar da zaman lafiya karkashin Majalisar Dinkin Duniya ke yi, aiki ne mai hadarin gaske da ke bukatar juriya, amma ya ce ya zama dole a yaki ta'addanci. Jamus na da akalla sojoji 170 a Mali. Ministan zai kammala ziyarar a ranar Alhamis