1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Murnar al'umar Libiya ta fara komawa ciki

August 27, 2012

Duk da zaɓen da aka shirya a Libiya har yanzu tsugunne ba ta ƙare ba dalili da tashe-tashen hankula

https://p.dw.com/p/15xR0
Source News Feed: EMEA Picture Service ,Germany Picture Service People sit during the National Transitional Council (NTC) handover ceremony of power to the national congress in Tripoli, August 8, 2012. Libya's ruling council handed over power to a newly elected national assembly on Wednesday in the North African country's first peaceful transition of power in its modern history but which comes amid heightened violence. REUTERS/Esam Al-Fetori (LIBYA - Tags: POLITICS)
Sabuwar Majlisar Dokokin LibiyaHoto: Reuters

Bayan kifar da mulkin shugaba Muhammar Kaddafi , al'umar ƙasar Libiya ta yi tsammanin shiga wani kykkyawan halin rayuwa ta fannin kwanciyar hankali, 'yanci, da wadatar tattalin arziki, to amma sannu a hankali, murna ta fara komawa ciki.Duk da cewar an yi nasara shirya zaɓen demokraɗiya na farko amma har yaanzu da sauran rina kaba wajen cimma burin da masu juyin juya halin ƙasar su ka sa gaba.

A duk cikin ƙasashen da al'uma ta ƙaddamar da juyin juya hali,buri da suka sa a gaba shine su samu cenji ta fannin inganci rayuwa fiye da yadda ta kasance a mulkin da suka kifar.

A ƙasar Libiya bayan da hamɓɓara da Muhammar Khadafi,shugaban ƙasar Faransa na wacen lokaci Nikolas Sarkozy, ya shirya taro na mussamman domin tunanin yadda gamayyar ƙasa da ƙasa za su taimakawa Libiya ta murmure daga yanƙi ta kuma shimfiɗa inganttacen tsarin demokraɗiya da tattalin arziki.

Haka zalika Jamus da sauran ƙasashen yammacin duniya sun bada goyan baya ga wannan mataki.

A wannan fannin Libiya ta shirya zaɓen 'yan majalisar farko na tarihi, kuma ta girka sabuwar Majalisa,to amma yadda al'amura ke tafiyar hawainiya,a halin yanzu ya kama da karin maganar malam bahaushe mai cewa "na rumtse ido ban ga kyan makamta ba" kamar yadda Jochen Hippler wani masani kimiyar siyasa dake jami'ar Duisburg ta Jamus ya yi nazari:

epa02987461 Libyan new interim Prime Minister Abdel-Rahim al-Kib speaks to reporters in Tripoli, Libya, 31 October 2011. Engineer Abdel-Rahim al-Kib won 26 votes in the 51-member council to head a new government, a council spokesman said, adding that he would appoint a cabinet in the coming days. EPA/SABRI ELMHEDWI
Abdel-Rahim al-Kib shugaban gwamnatin LibiyaHoto: picture-alliance/dpa

"Babban aikin dake gaban wannan sabuwar Majalisa da aka girka shine samar da cikkakar ƙasa wadda za ta kula da duk al'amuran dake wakana a cikin iyakokinta.Cimma wannan mataki na buƙatar ɗinke duk wata ɓarakar da ta kunno kai tsakanin ɓangarori daban-daban na al'umar da ke raye a cikin ƙasar".

Dabra da hakan, akwai batun farfaɗo da tattalin arzikin Libiya, wanda yaƙi yayi wa kaca-kaca, kuma duk wannan ba zai samu ba, face cikin yanayin kwanciyar hankali, saboda haka, har yanzu da sauran tafiya a ƙasar Libiya. A faɗin ƙasar baki ɗaya ƙungiyoyin sa kai ɗauke da makamai na kai hare- hare a wurare daban-daban.Sannan ƙasar na ƙara tsunduma cikin bambance-bambancen addini da ƙabilanci.Shin cikin wannan yanayi ko ƙasar Libiya za ta iya cimma tudun dafawa:

Jochen Hippler ya yi nazari akai:

" A ganina nan da shekara guda zuwa shekaru biyu ba mamaki a samun haɗin kan al'umar ƙasar ,to amma ya danganta da yadda da sabin magabata za su ɓullo ma al'amarin.Cilas ne ɓangarori masu gaba da juna su fuskanci juna, ta haka ne kawai za a iya samun nasara."

epa03370556 (FILE) A file phtograph dated 12 February 2012, shows Libyan interim Interior Minister Fawzi Abdelali speaking during a news conference in Tripoli, Libya. According to media reports on 26 August 2012, Abdelali resigned from his position after scathing criticism about security forces' handling of an upsurge of violence in the country. The resignation came shortly after an emergency meeting of the newly elected National Congress on security breakdowns in several areas of Libya. EPA/SABRI ELMHEDWI +++(c) dpa - Bildfunk+++
Fawzi Abdelali ministan cikin gidan Libiya da yayi murabusHoto: picture-alliance/dpa

Makonni biyu da suka gabata, an zaɓi Abdel Rahim el-Kib matsayin saban Firaministan ƙasar da kuma Mohammad al-Magarief a matsayin shugaban Majalisa. Babban ƙalubalen dake gaban wannan hukumomi shine ɓullo da saban kudin tsarin mulkin da zai samu karɓuwa daga jam'ar ƙasa.Haƙiƙa a cewar Hippler abin na da kamar wuya ta la'akari da halin da kasar ta shiga.Hatta shekaran jiya ministan cikin gida ɗaya daga shika-shikan gwamnati yayi murabus, abinda ke matsayin babban koma baya a yunƙurin tsarkake harkokin siyasar ƙasar.Sannan wani saban rikici n shine yadda masu tsatsauran kishin addinin islama suka fara wargaza kaɓurburran shehunnai.

Mawallafa: Thobis / Yahouza
Edita: Saleh Umar Saleh

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani