1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta nuna fargabar ta kan halin da ake ciki a Ukraine

April 25, 2014

A wata fira da tayi ta wayar talho da shugaban Rasha, shugaban gwamnatin Jamus ta nuna fargabarb ta kan abubuwan dake wakana a gabacin Ukraine.

https://p.dw.com/p/1BoZo
Atomgipfel Merkel 25.03.2014
Hoto: Reuters

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nuna Fargabar ta, dangane da halin da ake ciki a kasar Ukraine. Merkel din tayi wannan furuci ne yayin wata fira ta wayar talho da tayi da Shugaban kasar Rasha Vladimir Poutine a cewar kakakin gwamnatin ta Jamus Steffen Seibert yayin wani taron manema labarai a birnin Berlin, a wannan Juma'a (25.04.2014).

Mai magana da yawun gwamnatin ta Jamus ya kara da cewa abubuwan dake wakana a gabacin Ukraine na razanarwa sosai, kuma abubuwan da suka wakana tun daga taron Geneva, basu bada kwarin gwiwa, musamman ma daga bengaren Rasha, inda yace babu wani cigaba da suke gani, yayin daga bengaran Ukraine suka dukufa wajan aikata abubuwan da yarjejeniyar ta cimma.

Sai dai kuma a wata sanar wa da fadar shugabar gwamnatin ta bayar, tace a ranar 1 da ran biyu ga watan Mayu mai zuwa ne dai, Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel zata gudanar da wata ziyarar aiki a kasar Amirka.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu