1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mauritaniya za ta miƙa Al Senussi ga mahukuntan Libiya

March 22, 2012

Gwamnatin Mauritaniya ta ce za ta mika tsohon jami'in leken asirin Libiya ga mahukuntan kasar domin ya fuskanci shar'ia.

https://p.dw.com/p/14Osm
FILE - In this Sunday, Aug. 21, 2011 file photo taken on a government-organized tour, Abdullah al-Senoussi, head of Libyan intelligence, speaks to the press as gunfire erupts all around the Rixos hotel in Tripoli, Libya. The Libyan information minister says Moammar Gadhafi's intelligence chief has been captured by revolutionary fighters in the south of the country. Mahmoud Shammam says that Abdullah al-Senoussi was captured alive on Sunday by a brigade from a southern region called Fazan.(Foto:Dario Lopez-Mills, File/AP/dapd)
Abdullah al SenussiHoto: dapd

Ƙasar Mauritaniya ta ce za ta mika daya daga cikin mukarraban tsohon shugaba Libiya, Muammar Gadhafi wato Abdullah Senussi da ya yi aiki a matsayin babban jami'in leken ga kasar Libiya domin ya fuskanci shari'a a kasarsa ta haifuwa. Kakakin gwamnatin Maurtaniya Nasser Al Manei ya ce kasar ta amince da mika Al Senussi ga mahukuntan Libiya saboda a yi masa shari'a ta adalci. A karshen makon da ya gabamma har yanzu ba a tatance ranar da za a mika shi ga Libiya ba. Shi dai tsohon jami'in leken asirin na Libiya ba ma mahukunatan Libiya ne kadai ke nemansa ruwa ajallo ba, kasar Faransa da kotun hukunta miyagun laifuka ta kasa da kasa da ke da mazauninta a birnin the Hague na kasar Holland su kuma sun ba da sammace akansa. Ana zarginsa ne da laifin cin zarafin farar hula a lokacin da aka shiga boren nuna adawa da gwamnati a shekarar 2011 da kuma kashe firsinoni kasar ta Libiya guda 1200 a shekarar 1996.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita:Muhammad Nasiru Awal