1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Tasirin kafar sada zumunta ga matasan Kenya

Muntaqa Ahiwa Josey Mahachi/SB
August 20, 2024

Kafar sadarwar Internet ta sauya al'amuran rayuwa da suka shafi duniya kusan ta kowace fuska a wannan zamani. Baya ga hukumomi da kamfanoni, matasa kan yi amfani da internet matukar gaske, wajen biyan bukatu kala-kala.

https://p.dw.com/p/4jhRw
Matasan Kenya masu zanga-zanga a birnin Nairobi
Matasan Kenya masu zanga-zangaHoto: Boniface Muthoni/Sopa/Zuma/picture alliance

 

 

Kafar sadarwar Internet da ta zamo tamkar hanta da jini a rayuwar al'umar duniya a yau, fasaha ce da ta faro cikin shekarun 1960, inda a lokacin jami'an gwamnati ke musayar bayanai ta hanyar amfani da injuna masu kwakwalwa, sannan ake daukar ranar daya ga watan Janairun shekara ta 1983, a matsayin ranar kafuwarta a hukumance. Kafin samar da Internet a lokacin dai, kwamfutoci a duniya ba su da hanyar da suke iya aika wa juna da bayanai ko kuma musaya a tsakanin juna.

Karin Bayani: Babban sufeton 'yan sandan Kenya ya yi murabus

Kenya | Matasan Kenya masu zanga-zanga a birnin Nairobi
Matasan Kenya masu zanga-zangaHoto: TONY KARUMBA/AFP/Getty Images

A shekara ta 1986 akwai sama da kwamfutoci dubu biyar da suke aiki da hanyar sadarwar internet. Adadin ya matukar karuwa zuwa miliyoyi a lokacin da manyan makarantu da masu harkokin kasuwanci suka rungumi fasahar sadarwar ta Internet. A shekarun 1990 Internet ta yi matukar yaduwa a fannoni dabam-dabam na duniya har ta kai halin da ake ciki a yanzu da a wasu kasashen masu bore da sauran nau'uka na zanga-zanga ke cin moriyar Internet fiye da yadda ake tunani.

Watanni biyu da suka gabata, duniya ta shaida gagarumar zanga-zangar adawa da gwamnati a kasar Kenya bayan aniyar samar da dokar sauye-sauye da ke da nasaba da kudaden haraji. Kungiyar matasa ta Zoomer Generation ko kuma Gen Z a takaice. Wasu dai na mai ra'ayin cewa abin da ya faru a Kenya, na kama da batu da ya samu goyon bayan wasu masu karfi daga gefe, walau na ‘yan adawa ko kuma kungiyoyi na kwadago.