Matasa a zaben Najeriya na 2019
Wasu daga cikin matasan Najeriya sun baiyana jin dadinsu kan shiga harkokin zaben kasar, wannan shi ne karon farko da suke kada kuri'a a zaben da Shugaba Muhammadu Buhari ke neman wa'adin mulki na biyu:
Qudus Ayinla Rasheed zai yi zabe a karon farko
Qudus Ayinla Rasheed, dan shekaru 20 da haihuwa, zai gudanar da zabe a karon farko, Rasheed da ke zaune a jahar Kwara, ya ce fatan sa shi ne, kada kowa ya kuskura ya sayar da kuri'arsa, ya ce da kyau kowa ya zabi shugaban da zai shawo kan matsalolin Najeriya, amma ya fi mayar da hankali a yaki cin hanci da rashawa.
Oluwasegun Oladoke David dan shekaru 22
Oluwasegun Oladoke David, dan shekaru 22 da haihuwa, wannan shi ne karon farko da zai kada kuri'arsa a zaben na 2019.Oluwasegun ya ce yana fatan ganin an sami shugaba na gari. Ya na da kyau mutum ya kada kuri'arsa ga wanda ya ke so, ya na kuma son ganin duk wanda ya lashe zaben, ya inganta sashen ilimi da tsaron kasa da kuma karfafawa matasa guiwa da kuma son wasannin.
Kaka Adams Feyisola dan shekara 20
Kaka Adams Feyisola dan shekara 20, dalibi ne da ke shirin kada kuri'arsa a karon farko. Mazaunin jahar Legas, na son ganin an gudanar da zabe sahihiya da fatan ganin an tabbatar da tsaro don kare rayuwan al'umma. Ya ce ya shirya yin zaben don ya san kuri'arsa ce 'yancinsa. Ya na son duk wanda ya ci zaben, ya samar ma matasa aiki da ilimi kyauta tare da inganta fannin lafiya.
Caesar Kelechi Nlemoha dan shekara 21
Caesar Kelechi Nlemoha dan shekara 21 da ke a Abuja, ya ce yana da mahinmanci kowa ya fita don kada kuri'arsa don kuwa da haka kadai za a iya samun sauyi a kasa.Caesar na fatan ganin sabuwar Najeriya, inda duk wanda ya lashe zaben, zai farfado da tattalin arzikin kasa tare da inganta rayuwar jama'a dama fannin ilimi.
Noimot Shuaibu Ajoke yar shekara 18
Noimot Shuaibu Ajoke da ke zaune a jahar Kwara, ta ce wannan shi ne karon farko da za ta kada kuri'arta, fatan ta shi ne, a sami shugaban da zai kawo sauyi daga halin da ake ciki yanzu. Noimot na son ganin an zabi wanda ya fi dacewa, wanda zai taimakawa Najeriya a fannoni daban-daban.
Wasinu Lazarus dan shekaru 21
Dalibi Wasinu Lazarus mai shekaru 21, ya ce karon farko kenan da ya sami daman da zai kada kuri'arsa. Mazaunin jahar Legas da ke aikin tukin kwalekwale, ya ce, abin alfahari ne gare shi da ya sami damar gudanar da zaben. yana kuma fatan ganin jama'a sun zabi wanda ya dace da mukamin shugaban kasar.
Azonmayon Moses dan shekara 21
Azonmayon Moses dan shekara 21, malamin makaranta ne a wata unguwa ta marasa galihu da ke a jahar Legas, ya ce yana fatanwanda zai yi nasara ba zai aiwatar da umarnin rushe musu muhallinsu ba.Ina son shugaban da zai ban wannan tabbacin. Ya ce ba ya son gwamnati mai ci don ganin halin kunci na rayuwa da suke fama yanzu. Cin abinci kadai, abu ne mai wuya, shi yasa bama son ya dawo.