Maroko ta amince da bankunan Islama
January 4, 2017Kasar Maroko ta kasance kasa mai mafi rinjaye na Musulmi a baya-bayan nan da ta amince da kafa bankunan Musulinci, abin da ke zuwa bayan da a kasar a ke samun karuwar wadanda ke son amfanin da bankunan masu bin tsari na Shari'ar Islama.
Babban bankin kasar ta Maroko ya bayyana a wannan mako cewa ya amince da kafa irin wadannan bankuna guda biyar a wani bangare na cika alkawarin shekarar 2011 da jam'iyyar Islama ta PJD mai kwance da wasu wajen kafa gwamnatin kasar ta bayyana.
Cikin bankunan da za a fara aiwatar da tsarin na bankin Islama a cikinsu akwai babban bankin nan na Attijariwaf da ke da alaka da gidan sarautar Maroko da Banque Centrale Populaire da bankin BMCE mai zaman kansa , bankuna masu karfi a wannan kasa, sauran su ne bankin CIH da Credit Agricoledu Maroc. Bankuna hudu cikin wadannan za su yi aiki tare da bankunan na Moroko da cibiyar kula da hada-hadar kudi ta kasashen yankin Gulf, kamar yadda babban bankin kasar ya bayyana.