1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Marhabin da sakamakon zaɓen Libiya

July 18, 2012

NATO, wadda ta jagoranci kifar da gwamnatin tsohon shugaban Libiya Ghadafi ta yaba da zaɓen ƙasar, wanda ƙawancen jammiyun masu sassaucin ra'ayi ke kan gaba.

https://p.dw.com/p/15Zen
Mahmoud Jibril, Prime Minister of Libya speaks to reporters during the 66th United Nations General Assembly at UN Headquarters Friday, Sept. 23, 2011. (ddp images/AP Photo/David Karp)
Mahmoud JibrilHoto: AP

A cikin wata sanarwar da sakatare janar na ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO Anders Fogh Rasmussen ya fitar a wannan Larabar ya bayyana sakamakon zaɓen majalisar dokokin Libiya a matsayin wani muhimmin mataki a shirin da ƙasar ke yi na komawa bisa tafarkin dimoƙraɗiyya cikin kusan shekaru 50 da suka gabata.

Rasmussen ya ce ƙungiyar na yin alfahari da irin rawar da taka tare da sauran ƙawayenta wajen kare al'ummar Libiya a ƙarƙashin ƙudirin Majalisar Ɗinkin Duniya yayin da suka jagoranci gangamin kawar da mulkin Gaddhafi a shekarar da ta gabata, yana mai cewar a shirye ƙunigyar NATO take ta amsa buƙatar tallafawa sake gina ƙasar ta Libiya.

Shima firaministan wucin gadi na ƙasar ta Libiya AbdurRahim el-Keib irin wannan farin cikin ne ya bayyana game da sakamakon zaɓen na Libiya:

" Ya ce Lokaci ne na gudanar da shagulgula. Al'ummar Libiya ta yi rawar gani, kuma 'yan Libiya sun tabbatar da cewar suna da hazaƙar da a baya ba'a ba su damar nunawa ba, kuma hakan manuniya ce ga irin wayewar da da 'yan Libiyar ke da ita."

A woman with her fingers painted with colors of the pre-Moammar Gadhafi flag, flashes a victory during a demonstration against Gadhafi at the Green Square in Tripoli, Libya, late Tuesday, Aug. 30, 2011. Libyan rebels say they're closing in on Gadhafi and issued an ultimatum Tuesday to regime loyalists in the fugitive dictator's hometown of Sirte, his main remaining bastion: surrender this weekend or face an attack. (ddp images/AP Photo/Alexandre Meneghini)
Hoto: AP

            Jam'iyyun dake kan gaba a zaɓen Libiya

Sakamakon zaɓen majalisar dokokin Libiyar dai ya nuna cewar ƙawancen jam'iyyun dake da sassaucin ra'ayi a ƙarƙashin jagorancin tsohon firaministan wucin gadin Libiya Mahmoud Jibril ne suka sami kujeru 39 cikin adadin kujerun 'yan majalisa 80, yayin da jam'iyyar masu ra'ayin Islama ta Justice and Construction Party kuwa ta samu kujeru 17, kana sauran ƙananan jam'iyyu kuwa suka tashi da ragowar kujerun kamar dai yadda sakamakon wucin gadin da hukumar zaɓen ƙasar ta fitar ya nunar, abinda kuma wani ɗan Libiya mai suna Ahmed dake bayyana ra'ayin sa akan sakamakon zaɓen ya ce ya dace da hasashen da aka yi tunda farko:

" Ya ce tun asali ma irin wannan sakamakon ne muke sa ran samu domin kuwa Mahmoud Jibril yana da siffofin jagotanci kuma yana da ƙwarewa, saɓanin 'yan Uwan mu na jam'iyyr 'yan Uwa Musulmi waɗanda ba su da ƙwarewar da aka taɓa gani a ƙasa."

                  Fasalin majalisar dokokin Libiya

High National Election Commission workers check ballot boxes after collecting them from different polling stations as they prepare for the final count, in Benghazi July 8, 2012. Nine months after Muammar Gaddafi's death at the hands of rebels, Libya has defied fears it would descend into violence by pulling off a largely peaceful election, its first national and free vote in 60 years. REUTERS/Esam Al-Fetori (LIBYA - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Masu jefa ƙuri'a a zaɓen LibiyaHoto: Reuters

Sai dai kuma sakamakon zaɓen ba zai kasance tabbaci ne ga ɓangaren da zai sami rinjaye a majalisar dokokin Libiya ba domin kuwa a ƙarƙashin dokokin zaɓen, an keɓe kujeru 120 ne ga ga ɗai-ɗaikun 'yan takarar da za'a zaɓa nan gaba, inda a yanzu manyan jam'iyyu biyu dake sahun farko ke zawarcin ƙananan jam'iyyu da kuma 'yan takara masu zaman kansu da nufin samun rinjaye a majalisar dokokin da Libiya ke ka hanyar samu, wadda a cikin ta mata za su sami kaso 16 da rabi cikin 100 na ɗaukacin kujeru 200 da majalisar dokokin ke da su, wato aƙalla mata 30 ne za su shiga majalisar, lamarin da wai ɗan Libiya ya ce zai yi tasiri ga makomar ƙasar:

" Ya ce yana da muhimmancin gaske ga makomar ƙasar, kuma ina ganin 'yan Libiya na hanƙoron ganin cewar sakamakon wannan zaɓen zai taimaka wajen girka kyakkyawan tsarin dimoƙraɗiyya a ƙasar da kuma samar da shugabanni na gari da za su jagorance ta."

Sabuwar majalisar dokokin Libiyar dai na da alhakin kafa sabuwar gwamnatin wucin gadin da za ta tafiyar da lamuran ƙasar na kimanin shekara guda, gabannin gudanar da wani sabon zaɓen da zai dogara akan sabon tsarin mulkin da majalisar za ta samar.   

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita: Halima Balaraba Abbas