1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar al-Maghrahi a rikicin Libiya

August 29, 2011

Majalisar wucin gadin Libiya ta ce ba za ta miƙa Abdulbaset al-Maghrahi ga Scotland ba bisa laifin ɗana bom a cikin jirgin saman Amirka a shekarar 1988

https://p.dw.com/p/12PYl
Abdel Baset al-Megrahi, a tsakiya yayin saukarsa a Libiya daga ScotlandHoto: AP

Balibiyen nan da aka ɗora wa laifin kai hari ma wani jirgin saman Amirka a sararin samaniyar garin Lockrbie na ƙasar Scotland a shekarar 1988 wato Abdulbaset al-Maghrahi yana cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai. To amma majalisar wucin gadin ƙasar ta Libiya ta ce ba za ta miƙa shi ga ƙasar ta Scotland inda ya shafe shekaru takwas yana zaune a gidan yari kamar yadda wasu daga cikin iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a cikin hari suka buƙata ba. Al-Maghrahi an yanke masa hukunci ne bisa laifin ɗana bom cikin jirgin saman Pan- Am da ya tarwaste a sararin samaniyar garin Lockerbie da fasinjoji 270 a cikinsa. A shekarar 2009 ne dai aka sake shi domin nuna masa jinƙai bisa fama da yake yi da cutar kansa wadda a sakamakonta aka ce zai mutu watannin uku bayan an sake shi. Ƙasar ta Scotlanda a nata ɓangaren tac e ba ta da niyyar miƙa buƙatar dawo mata da wannan mutun .

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mhammad Nasiru Awal