Chadi da Nijar za su ƙaddamar da hari kan Boko Haram
March 8, 2015Talla
Ƙungiyar ta Boko Haram dai na yin gwaggwarmaya da makamai a maƙwabciyar ƙasashen na Chadi da Nijar ɗin wato Tarayyar Najeriya. Majiyar ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na ƙasar Faransa na AFP cewar za su ƙaddamar da gaggarumin farmakin a yankin arewa maso gabashin Tarayyar Najeriyar da ƙungiyar take da ƙarfi wanda kuma ke kan iyaka da garuruwan Bosso da Diram. Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da aka kai wani mummunan hari a Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno a Tarayyar Najeriya tare da hallaka mutane sama da 50.