Libiya ta kori baƙi
November 27, 2013Talla
Ƙasar Libiya ta kori kimanin baƙi 'yan ci-rani daga ƙasashen Afirka 500. Kamfanin dillalcin labaran gwamnatin ƙasar ta Libiya, ya ce baƙin an tisa ƙeyarsu zuwa ƙasar Jamhuriyar Nijar ne, a wani matakin rage tuttuɗowar da baƙi yan ci-rani da kuma masu kaifin kishin Islama a ƙasar. Ƙasashen Yamma dai na gudun cewa, ƙasar Libiya za ta kasance wata tunga ga ƙungiyar Alƙa'ida, yayinda a yanzu gwamnati mai rauni ta ke neman kakkaɓe mayaƙa da ke ɗauke da makamai, kana da sauran matasan da aka yi amfani da su a yaƙin kifar da gwamnatin Gaddafi.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu