Zai saki matarsa shekaru 32 bayan aure
June 21, 2021Laurent Gbagbo ya ce bisa kin amincewa da yin rabuwa irin ta arziki, hakan tilasta masa shigar da takardar neman sakin matarsa a gaban wata kotu da ke birnin Abidjan. Masu 'ya 'ya biyu tun bayan daura masu aure a shekarar 1989, ma'auratan sun shafe tsawon shekaru 32 suna gwagwarmayar siyasa, kafin kama su a cikin watan Afrilun shekarar 2011 bisa zargin hannu cikin rikicin bayan zabe. A makon jiya an hango Laurent Gbagbo mai shekaru 76 a yayin da ya sauka filin jirgin saman Abidjan tare da wata tsohuwar 'yar jarida budurwarsa Nady Bamba, bayan kotun ICC ta wanke sa daga zargin aikata laifukan yaki. To amma kuma ko baya ga budurwarsa, an ga mai dakinsa Simone Gbagbo 'yar shekaru 72, tana zantawa da shi, kan daga bisani ta yi wa wurin batan dabo.