Karanci mai ya kusa durkusar da Najeriya
May 28, 2015Talla
Karancin man fatur da Najeriya ta fuskanta biyo bayan yajin aikin da dillan da ke dakon mai suka yi ya jefa Najeriya cikin mawuyacin hali. Lamarin dai ya jawo asara mai dimbin yawa ga 'yan kasuwa. Sai dai daga bisani gwamnati da dillalan man fetur din daidaita har ma sun koma dakon mai din kamar yadda aka saba.