1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta karɓi 'yan gudun hijira daga Libiya

September 4, 2012

Rukunin farko na 'yan gudun hijirar ƙasar Libiya kimanin 195 ne suka iso Jamus bayan kasancewa a ƙasar Tunisiya na tsawon shekara guda.

https://p.dw.com/p/1632x
Men from Bangladesh, who used to work in Libya and fled the unrest in the country, carry their belongings as they arrive in a refugee camp at the Tunisia-Libyan border, in Ras Ajdir, Tunisia, Wednesday, March 9, 2011. The 20,000-capacity transit camp for thousands of migrant workers who have fled the fighting in Libya in the past two weeks is about seven kilometers (four miles) from the Libyan border and is expanding with each day of crisis in Libya. (Foto:Lefteris Pitarakis/AP/dapd)
Hoto: dapd

Hukumomi a ƙasar Jamus sun yi marhabin lale da rukunin farko daya ƙunshi 'yan gudun hijirar Libiya, a matsayin wani bangare na shirin sake tsugunar da jama'ar na Majalisar Ɗinkin Duniya. 'Yan gudun hijirar da adadin su yakai 195, waɗanda suka isa filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Hannover da ke tarayyar Jamus a wannan Litinin, sun kwashe tsawon shekara ɗaya suna sansanin 'yan gudun hijirar da ke ƙasar Tunisiya. Galibin su kuma sun rasa matsugunan su yayin rikicin ƙasar ta libiya. Sai dai gabannin jigilar su zuwa Jamus, sun samu horon tsawon makonni biyu game da tsarin harshe da kuma na al'adun Jamusawa a ƙasar ta Tunisiya. Hakanan za su ɗauki tsawon makonni biyu a wani sansanin da ke nan Jamus domin sanin irin kalubalen rayuwar da ke gaban su. Bayan haka ne kuma za'a rarraba 'yan gudun hijirar zuwa wasu jihohin Jamus daban daban.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh
Edita : Zainab Mohammed Abubakar