Ignace Murwanashyaka ya mutu
April 18, 2019Talla
Ignace Murwanashyaka ya rasu a Jamus inda ake tsare da shi a gidan kurkuku inda yake jiran kotu ta sake duba hukuncin da aka yanke masa. Ignace Murwanashyaka wanda ya mutu a wani asibitin jami'ar Mannheim, dan kimanin shekaru 55 kotun ta ce ba ta da bayyanai a game da cutar da ta kasheshi saboda siri na likita. Tun farko kotun Karlsruhe ta yanke wa jagoran na kungiyar mayakan FDLR hukuncin daurin shekaru 13 a shekara ta 20015, bayan da ta sameshi da laifin ba da umurnin kai hare-hare a arewacin Kivu tun a shekara ta 1980.