1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mozambik: Jagoran adawa zai gana da shugaban kasar

November 23, 2024

Madugun adawa na kasar Mozambik ya amince da tayin tattaunawa da shugaban kasar ya yi masa, bayan mummunan rikicin da ya barke bayan babban zaben kasar.

https://p.dw.com/p/4nLk6
Mosambiks Präsidentschaftskandidat Venâncio Mondlane
Hoto: Alfredo Zuniga/AFP

Sai dai a faifain bidiyo na kai tsaye a shafinsa na Facebook, jagoran adawar Mozambik, Venancio Mondlane ya gindaya sharudda kafin ganawa da shugaban kasar saboda gudun tarkon siyasa, inda ya bukaci a gudanar da ita ta kafar bidiyo kuma a yi watsi da shari'ar da ake masa. Shugaba Filipe Nyusi ya aika goron gayyata ga dan adawa Venancio Mondlane ne bayan da gomman mutane suka rasa rayukansu, sakamakon murkushe masu bore da 'yan sanda suka yi a zanga-zangar adawa da sakamakon zaben 9 ga watan Octoban da ya gabata.

karin bayani: Zanga-zangar watsi da sakamakon zaben Mozambique

Ana dai kyautata zaton cewar Mondlane wanda ya yi zargi an tafka magudi a zaben ya tsere daga Mozambik, saboda gudun kame shi ko kai masa hari, amma har yanzu ba a san inda yake ba. Hukumomin kasar dai na zarginsa ne da laifuka da dama, ciki har da lalata dukiyoyin jama'a da magoya bayansa suka yi yayin zanga-zanga, lamarin ya haifar da toshe asusun ajiya na bankinsa.