Jadawalin zaɓe a Najeriya
March 16, 2010Talla
Hukumar zaɓen Nigeria, ta fitar da jaddawalin zaɓen
shugaban ƙasa na gaba. Hukamar ta INEC, tace imma
dai ayi zaɓen a ranar 22 ga watan janairun ko kuma
23 ga watan Aprilun baɗi. Da yake magana shugaban
hukumar ta INEC, wato Mauris Iwu, yace sun fidda
jadawali kashi biyu ne, kuma hakan sun yi shi ne
domin jiran tsammani a bisa abinda majalsar dokokin
ƙasar za ta zartar, a kuɗurin tsarin zaɓen ƙasar dake
gabanta. Mauris Iwu yace daga nan har izuwa watan
Augusta, ko nowamba, idan dai aka basu dokar, to za
su iya yin kwaskwarimar da ta kamata. Wannan
jadawalin dai ya kumshi zaɓen shugaban ƙasa da 'yan
majalisu da gwamnonin jihohi na tarayyar ƙasar. A
bisa dokar zaɓen ƙasar da ake anfani da ita a yanzu,
to sai watan Aprilun baɗi za ayi zaɓen shugaban ƙasa
na gaba, domin maye gurbin shugaba na yanzu wanda
wa'adinsa zai ƙare a watan mayun baɗi. Ƙudurin da ke
gaban majalisar dokokin ƙasar wanda kuma kwamitin
da Mai shari'a Muhammadu Uwaisu ta gabatar, ta
buƙaci da ayi zaɓen shugaban ƙasa watanni shidda
gabanin rantsarwa, domin baiwa mutanne dake ƙorofi
damar su kai ƙara kuma a yanke hukunci, kafin
rantsarwa, domin kaucewa giɓen da aka samu bayan
zaɓen shugaba 'Yar'adua, inda bayan rantsar da shi
har shekaru biyu ana ta kai kawo a kotu.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Yahouza Sadissou Madobi
Talla